Da DANGARI: Tarihin Garin Tunga, Jihar Nasarawa, Satumba 17, 2022

Badiagra, Mali

Shirin Da Dangari na wannan makon ya kai ziyara karamar hukumar Awe da ke jihar Nasarawa a Najeriya don jin tarihin masarautar Tunga.

Masarautar Tunga dai wani ne mai suna Mamman Angulu daga jihar Katsina ya kafa garin, a cewar mai martaba sarkin Tunga Alhaji Muhammed Ibrahim Shu'aibu a wata hira da Sadiq Abbas na gidan rediyon Jihar Nasarawa.

Kimanin shekaru dari da suka wuce aka kafa garin Tunga bayan da Mamman Angulu ya bar Katsina saboda an hana shi sarautar Galadima. A matsayinsa na maharbi, sai ya yi tafiya mai nisa zuwa jihar Nasarawa bayan ya yada zango a wurare dabamdaban.

Masarautar Tunga, wadda ta shahara a sana'ar noma da kiwo, na da gidajen sarauta uku, a cewar Alhaji Shu'aibu wanda shi ne sarki na tara. Ya kuma ce ana yi wa garin kirarin "Tsintsiya Madaurinki Daya."

Basaraken ya ce a shekarun baya kafin bude kamfanin Dangote, 'yan fashin daji da barayin dabbobi sune babban kalubalen al'umar garin, amma zuwan kamfanin ya sa an samu sauki.

Saurari cikakken shirin cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Da DANGARI: Tarihin Garin Tunga, Jihar Nasarawa