Shirin Da Dangari na wannan makon ya kai ziyara garin Tsagem da ke karamar hukumar Mani a jihar Katsina don jin tarihin garin.
WASHINGTON —
Garin Tsagem ya shahara sosai kuma gari ne na Fulani da Malamai. Basaraken garin Buhari Usman, ya ce garin ya shahara a fannin kiwo da noma kuma har yanzu kaburburan sarakunan garin na baya na nan a wurin Dutsen Gandu.
Duk da shahararsa, garin na fuskantar kalubalen karancin samun ci gaba, musamman ta bangaren hanyoyi da kuma karancin ruwa.
Saurari cikakken shirin wanda Abdul Jani ya gabatar.
Your browser doesn’t support HTML5