WASHINGTON, DC - Wakilin Muryar Amurka Mansur Sani ya yi hira da Alhaji Ali basaraken garin Takalmawa, wanda ya bayyana cewa sunan garin ya samo asali ne daga takalma, wato buga takalman kirgi. A lokacin baya, an yi yayin wadannan takalman sosai saboda yadda aka hadasu.
Ya ce wani mai suna Yarima da dansa Maigari (Sani), sune suka kafa garin. ‘Yan garin masu hazaka ne sosai, a cewarsa da suka shahara wajen buga takalma. Ya kara da cewa a baya, da wuya a ga masu zaman banza, kusan kowa na aiki.
Noma da kiwo na daga cikin ayyukan da al’umar Takalmawa suka yi sosai. Alhaji Ali ya ce a yanzu suna fuskantar kalubalen rashin hanyoyin ruwa kuma suna fatan gwamnati zata taimaka ta yi musu gyaran hanyoyin ta kuma gina musu kwalbati.
A karshe Basaraken ya yi kira ga matasa da jama’ar gari da su tashi tsaye su nemi na kansu don samun abun rufin asiri da gujewa zaman kashe wando.
Your browser doesn’t support HTML5