Da Dangari: Tarihin Garin Iggah, Jihar Nasarawa, Oktoba 1, 2022

A wannan makon, gidan rediyon jihar Nasarawa ya kai ziyara masarautar Iggah da ke jihar Nasarawa a Najeriya.

Sadiq Abbas na gidan rediyon jihar Nasarawa ya kai ziyara fadar masarautar Iggah da ke karamar hukumar Nasarawa Egon, inda ya yi hira da Sangarin Iggah na goma sha uku Idris Bonaa Ahmed.

Basaraken ya ce asalinsu Gwandari ne da suka fito daga Kano kuma bisa ga tarihi masarautar ta kafu ne kimanin shekara dari biyar da suka wuce.

Shi dai wannan gari ana yi mashi kirari da "Iggah turakar kifi," saboda shaharar da garin yayi wajen sana'ar kamun kifi.

Saurari cikakken shirin cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Da Dangari: Tarihin Garin Iggah, Jihar Nasarawa