DA DANGARI: Tarihin Garin Gazurawa Da Ke Birni N’Konni A Nijar, Maris 11, 2023

Bandiagara, Mali

A wannan makon Harouna Mammane Bako na gidan rediyon Niyya FM ya yi tattaki zuwa garin Gazurawa da ke yankin Birni N'Konni a jamhuriyar Nijar don jin tarihin garin.

Mai garin Gazurawa Garba Isah, ya ce tun a zamanin da turawan mulkin mallaka suka kwace N'Konni aka kafa garin Gazurawa.

Ya kuma ce noma da sana'a sune abubuwan da mazauna garin ke tunkaho da su, sai dai rashin tsaro wani babban kalubale ne ga harkar noma a lokacin damina. Malam Garba ya kuma ce garin na bukatar hanya daga N'Konni da kuma sabbin makarantu.

Saurari cikakken shirin:

Your browser doesn’t support HTML5

DA DANGARI: Tarihin Garin Gazurawa Da Ke Birni N’Konni A Nijar