DA DANGARI: Tarihin Garin Gadar Gayan, Jihar Kaduna, Yuni 11, 2022

Bandiagara, Mali

A wannan makon gidan rediyon Nagarta FM ya lalubo tarihin garin Gadar Gayan da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna a Najeriya.

WASHINGTON, DC - Kimanin shekaru dari da hamsin da suka wuce aka kafa garin Gadar Gayan, a cewar daya daga cikin dattawa kuma shugabannin garin, Mohammadu Shu’aibu Gadar Gayan.

Ya ce Gadar Gayan karamin gari ne da ke da albarkatun kasa musamman ta fannin noma, abinda ya sa kasuwar garin ta yi suna saboda yadda ‘yan kasuwa daga wasu jihohin Najeriya har ma da kasashen waje kamar Kamaru, Nijar, da sauransu ke zuwa cin kasuwa. Ita dai wannan kasuwa duk ranar Juma’a ake cin ta.

Garin na da duwatsu da kogi wanda ake amfani da shi wajen kamun kifi.

Sai dai duk da sunan da kasuwar garin ta yi ba ta da rumfunan zamani duk da harajin da 'yan kasuwa ke biya, a cewar Dattijo Mohammadu.

Saurari cikakken shirin da Nasiru Yakubu Birnin Yero ya hada.

Your browser doesn’t support HTML5

DA DANGARI: Tarihin Garin Gadar Gayan, Jihar Kaduna