DA DANGARI: Tarihin Garin Dargue Da Ke Jihar Maradin Jamhuriyar Nijar, Yuli 16, 2022

Bandiagara, Mali

A wannan makon Haruna Ibrahim Ras ya kai ziyara garin Dargue da ke karamar hukumar Jibiri a jihar Maradin Jamhuriyar Nijar.

WASHINGTON, DC - Daya daga cikin dattawan garin Alhaji Isouhou Jari, ya ce a shekarun baya garin Dargue na da itatuwa sosai kuma iccen Dirga ne ya fi yawa, mafarin asalin sunan garin Dargue kenan.

Kimanin shekaru dari da hamsin da biyar zuwa dari da sittin aka kafa garin Dargue a cewar dattijo Isouhou.

Garin dai ya shahara wajen kiwo da noma kuma Abzinawa da suka taso daga Agadas ne suka kafa garin, amma akwai sauran kabilu a garin da suka hada da Wangarawa, Addawa, Hausawa da sauransu.

Saurari cikakken shirn da Harouna Mamane Bako ya gabatar.

Your browser doesn’t support HTML5

DA DAN GARI: Tarihin Garin Dargue Da Ke Jihar Maradin Jamhuriyar Nijar