WASHINGTON, DC - Harouna Mamane Bako na gidan rediyon Niyya FM a Nijer, ya yi hira da hakimin garin Cerasa Gune Alhaji Hassan Gado don jin tarihin garin.
Alhaji Hassan dan shekara 70 da haihuwa, shi ne hakimin garin na goma, ya bayyana cewa wani da ake kira Adamu Gune ne ya kafa garin kimanin shekaru dari biyu da suka wuce.
Garin, wanda asali Hausawa ne suka kafa shi, ya shahara wajen yaki a cewar Hassan. Ya kuma kara da cewa a shekarun baya, sai duwatsun garin su hade a lokacin yaki ko kuma tafkin garin ya kafe, akan dole mayaka su koma.
Rashin hanyoyi masu kyau na daga cikin kalubalen da garin ke fuskanta a cewar Hassan. Amma malam Abdu Hamidu, magajin garin Birni N’Konni, ya ce suna sane da wannan matsalar kuma in Allah ya yarda zasu dauki mataki nan ba da dadewa ba.
Saurari cikakken shirin cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5