A wannan makon gidan Rediyon Niyya FM da ke Birni N'Konni a jamhuriyar Nijer ya kai ziyara garin Bazaga.
Washington, DC -
Wakilin muryar Amurka Harouna Mammane Bako tare da Mousa Arzouka sun yi hira da wani dattijo mai suna Musa Ibrahim wanda ya bada dan takaitaccen tarihin garin. Ya ce kimanin shekaru 100 da suka wuce aka kafa garin.
A cewarsa, garin yana bace wa abokan gaba a lokutan yaki abinda ya sa da wahala a ci garin da yaki a baya.
Rikicin makiya da manoma na daga cikin matsalolin da mazauna garin ke fama da su a cewar Dattijo Ibrahim.
Saurari cikakken shirin cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5