A wannan makon shirin Da Dan Gari ya kai ziyara garin Ugah da ke jihar Nasarawa a yankin tsakiyar Najeriya don jin tarihin masarautar garin.
WASHINGTON, D.C —
Dagacin garin Ugah da ke karamar hukumar Lafiya, Alhaji Abdulkarim Yusuf Ubandoma, ya ce bisa ga tarihi tun a karni na 13 aka kafa garin Ugah. Shi dai wannan gari ya shahara a sana'ar farauta da kamun kifi, a cewarsa.
'Yan kabilar Akye su ne suka kafa garin Ugah a cewar dagacin, kuma su ke sarautar garin.
Saurari cikakken shirin da Sadiq Abbas ya gabatar.
Your browser doesn’t support HTML5