Shirin Da Dan Gari na wannan makon, wanda gidan rediyon Niyya FM ya gabatar, ya kai ziyara garin Kwara a jihar Tahoua don jin tarihin sa.
WASHINGTON, DC —
Garin Kwara mai tazarar kilomita kimanin 50 gabas da birnin Illela, na da yawan al'umma kusan dubu hudu zuwa dubu biyar.
Alhaji Isah Musa, daya daga cikin dattijan garin, ya ce asali mutanen garin Kwara daga Maradi suka fito kuma galibi hausawa da fulani ne ke zama a wannan garin.
A wata hira da wakilin Muryar Amurka Harouna Mamane Bako, Isah ya ce ya zuwa yanzu an sami mutun 16 da suka rike mukamin Magajin gari a Kwara kuma garin ya yi suna wajen farauta da martaba.
Saurari cikakken shirin daga Harouna Mammane Bako.
Your browser doesn’t support HTML5