Da Alamun Samun Nasara A Yakin Sake Kawar Da Ebola

Shugabar hukumar kiwon lafiya ta duniya a nahiyar Afrika, ta rawaito cewar a kwai alamomi masu kwantar da hankali wurin yaki da yaduwar cutar Ebola a Demokaradiyar Jamhuriyar Congo.

Matshidiso Moeti ta fadawa Muryar Amurka cewar suna sane da wasu kalubalen dake tattare da barkewar cutar na baya bayan nan, sai dai tace sun samu kwarin gwiwa ga yadda gwamnati da kawayenta na cikin gida da kasashen waje suka gaggauta daukar mataki a wannan lokacin.


Tace tana kyautata zaton samun nasara saboda wannan gwamnati tana da sani a kan wannan abu, da kuma yadda ta yi gaggawa wurin daukar mataki tare da kawayenta da suke aiki tare.

Moeti ta kara da cewar, suna samun taimakon kayan aiki daga shirin abinci na duniya da kuma wurin Majalisar Dinkin Duniya, don haka akwai kwarin guiwa a wannan aiki.

Hukumar ta WHO tace akwai labarin mutane 29 da ake zaton sun kamu da cutar ta Ebola ciki mutane uku sun mutu, tun lokacin da aka gano cutar a wani yankin karkara a DR Congo a ranar 22 ga watan Afrilu.