Tsagaita wuta a Syria ta fara aiki gadan gadan a ranar Talata a yayin da aka samu rahotonnin lafawar al amurra da kuma tarzoma.
WASHINGTON DC —
Da faduwar ranar jiya Litinin aka kaddamar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta. Sa’oi bayan kaddamar da yarjejeniyar, sataren harkokin wajen gwamnatin Amurka John Kerry ya ayyana cewa kila wannan itace dama ta karshe da za’a iya ceton kasar da ga yakin basasar shekaru biyar.
John Kerry yace kada a yi garaje wajen tantance ingancin yarjejeniyar, wadda Rasha da Amurka suka shiga Tsakani aka kulla.
John Kerry ne da Ministan Harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov suka bayyana cimma yarjejeniyar da sanyin safiyar Asabar a Geneva. Sannan yarjejeniyar ta samu goyon bayan wasu kasashe wadanda suka hada da Iran wacce take goyon bayan gwamnatin Syria, da kuma Turkiya wacce ke bukatar cire Al assad daga karagar mulki.