Zika Ta Kashe Mutum Na Farko A Amurka.

Dr. Thomas Friedon darektan cibiyar hana yaduwar cututtuka.

Mutumin dan shekaru 70 da haifuwa a watan febwairu ne ya kamu d a cutar da Zika.

A karon farko a Amurka, an sami mutuwa da ake dangnatawa da zazzabin cizon sauro da ake kira Zika.

Jami'ai a cibiyar hana yaduwar cututtuka ta Amurka, suka bada rahoton cewa wani mutum dan shekaru 70 da haifuwa daga yankin Puerto Rico, ya gamu da ajalinsa sakamkon yoyon jini cikin jikinsa da cutar da ya kamu d a ita a karshen watan biyu ta haddasa.

An sami mace mace uku masu kamada irin wannan a kasar Columbia.

Yankin Puerto Rico yana fuskantar barkewar cutar ta zika cikin watannin nan. Cibiyar hana yaduwar cututtukan, ta bada rahoton cewa,bincike ya nuna cewa an tabbatar mutane 683 sun kamu da cutar tsakanin daya ga watan Nuwamba zuwa 15 ga wannan wata. Akalla 65 daga cikin wannan adadi, mata ne mas juna biyu. An kwantarda mutane 17 a asibiti domin jinya.

Ba safai ake samun mace mace tsakanin maza domin kamuwa da wannan cuta ba, galibi tana janyo 'yar rashin lafiya na wani dan gajeren lokaci. Sai dai mata masu juna biyu da suka kamu da cutar tana janyo mutuwar abunda take dauke da shi, ko kuma lahani ga kwakwalwa, wanda ya janyo damuwa ta fuskar kiwon lafiya a duk fadin duniya.