Gwamnatin jihar Eboyin ta ce an samu gagarumin ci gaba a yunkurin dakile cutar zazzabin Lassa wadda ya yi sanadiyar mutuwar mutane hudu da suka hada da likitoci biyu a makon jiya.
Gwamnatin, yanzu ta bada umurnin sake bude makarantun da aka rufe sanadiyar barkewar cutar a duk fadin jihar. Mr Emmanuel Uzor dake magana da yawun gwamnatin jihar ya shaidawa Muryar Amurka hakan yau Laraba.
Mr Uzor ya ce an rufe makarantun ne domin baiwa jami'an kiwon lafiya na jiha da na tarayya damar tsaftace harabobinsu da sinadirai masu kashe kwayoyin cuta. Bayan an tsaftacesu ne kwararru suka bada shawarar a sake bude makarantun.
Akan kokarin da gwamnatin jihar ke yi na tabbatar da cewa ba'a sake samun barkewar cutar ba, kakakin gwamnati ya ce bayan barkewar cutar gwamnati ta gano cewa dan kwangilan da ta ba gina cibiyar binciken cututtuka bai kammala ba sai ta kafa kwamitin bincike lamarin da ya kaiga dawo da dan kwangilar har sai da ya cika cibiyar da kayan aiki.
A cewar Mr Uzor yanzu an samu saukin cutar saboda babu wani sabon rahoton cewa wani ya kamu da ita. Kazalika hukumomin kiwon lafiya na ci gaba da binciken kwakwaf akan mutane 123 da ake zaton watakila suna dauke da kwayar cutar. Amma naurorin gwaji sun nuna mutane 100 cikinsu basa dauke da kwayar cutar.
Ga rahoton Alphonsus Okoroigwe da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5