Cutar Sankarau Ta Bulla Jamhuriyar Nijer

Hukumomin kiwon lafiyar al’uma a jamhuriyar sun sanar cewa an sami bular kwayar cutar sankarau a wasu daga cikin yankunan kasar inda mutane 11 suka rasu daga cikin mutanen 109 da suka kamu da wannan cuta.

Ministan kiwon lafiyar al’uma Dr Iliyasu Idi Mainasara, ya bayyana cewa kawo yanzu matsalar bata kai mizanin annoba ba domin kuwa an dauki matakan dakile bazuwar wannan cuta.

Ministan ya kara da cewe ana yawan samun bullar wannan cuta a kasashen Kamaru, Najeriya, Burkina Faso, Benin, Nijer da sauransu a kusan kowace shekara, amma wannan karon lamarin yazo da sauki, domin kuwa kusan dukkan sauran kasashen da ya zayyana za a iya samun bangarori akalla hudu dake fama da wannan cuta amma a jamhuriyar Nijer, Allah ya takaita lamarin.

Ya kara da cewa ana samun wadanda suka kamu da cutar jefi-jefi amma ba kamar yadda za a kwatanta shi a matsayin annoba ba, wajibi ne a yaba rawar da ma’aikatar lafiyar kasar da kungiyoyi masu taimakawa Nijer, suka taka na samar da magunguna a fadin kasar.

Daga Jamhuriyar Nijer, ga rahoton Suleman Mumuni Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

Cutar Sankarau Ta Bulla Jamhuriyar Nijer