Kawo yanzu fiye da kaji dubu goma ne cutar ta halaka a gonaki shida dake cikin jihar ta Filaton Najeriya.
Cutar na shafar tsuntsaye nauin kaji da talotalo da dai sauransu. Cutar tana kisan tsuntsayen cikin hanzari.
Wata mai kula da lafiyar dabbobi a jihar tace sun hallaka kaji fiye da dubu goma agonaki shida da zummar dakile yaduwar cutar. Ta kara da cewa akwai wasu gonaki biyu dake da kaji dubu goma da ake zaton sun kamu da cutar. Tace yanzu suna kan wayarwa masu kiwon kaji kai.
Gwamnatin jihar ta kira masu kiwon kaji kada su sayar da kajin da suka kamu da cutar domin kada cutar ta dinga yaduwa. Ta kuma basu shawara su dinga tsaftace gonakansu.
Mr John Dafar shugaban kungiyar masu kiwon kaji ta Najeriya reshen jihar Filato yace masu kiwon kaji a jihar sun tafka asara. Ko shekakrar da ta gabata sun yi hasarar kaji kimanin dubu dari hudu. Yanzu kuma sai gashi cutar ta sake bullowa.
Ya roki gwamnati da ta taimaka masu da magungunan kashe kwayar cutar tare da bukatar gwamnati ta taimaka da biyan diya domin ya ragemasu hasara..
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5