Cutar Lassa Ta Kara Bullowa a Najeriya

Ana ci gaba da samun bullar cutar zazzabin Lassa a wasu sassan Najeriya, abinda ya sa hukumar NCDC fidda sanarwa akan halin da ake ciki.

Wannan sanarwar na zuwa ne daga hukumar yaki da yaduwar cututtuka ta Najeriya da ake kira NCDC a takaice, hukumar tace mutune 60 sun kamu da cutar a jihohi 8 daga farkon shekarar nan zuwa yanzu.

Hukumar ta NCDC tace ta kafa wani kwamiti dake da wakilai daga hukumar lafiya ta duniya da sauran masu ruwa da tsaki domin shawo kan lamarin. Dr. Sani Gwarzo dake aiki da ma'aikatar lafiya ta tarayya yace abin tada hankali gameda cutar Lassa shi ne yadda ba a iya bambamce ta da wasu cututtukan kamar masassarar cizon sauro da makamantansu. Shi yasa yake da muhimmanci duk wanda ya fara jin alamun masassara ya garzaya zuwa wurin likita don a tantance abinda ke damunsa, a cewar Dr. Sani.

Dr. Sa'idu Ahmad shine mataimakin babban darakta na ma'aikatar lafiya ta Najeriya ya ce an dauki matakan shawo kan cutar. Yace dama makasudin bude hukumar ta NCDC kenan don magance yaduwar irin wadannan cututtukan.

Bincike dai ya nuna cewa cutar zazzabin Lassa tafi kamari ne a lokacin zafi kuma cutar tayi tsanani ne a najeriya a shekara ta 2018.

Ga labari cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Cutar-lassa-ta-kara-bullowa-a-najeriya - 2'55"