An tabbatar da bullar cutar kyenda a kananan hukumomi goma sha hudu daga cikin goma sha shida dake jihar Taraba da ya yi sanadiyyar macemacen yara da dama ‘yan kasa da shekaru goma.
Babban jami’in asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya, MDD, a jihar Taraba Dokta Zarto Philip ya sanar da haka a wani taron gaggawa da shugabannin kananan hukumomi, sarakunan gargajiya da jami’an kiwon lafiya mataki na farko gabannin soma aikin rigakafin cutar kyenda a jiha.
Dokta Zarto Philip ya ce a jihohin arewa maso gabas yara dari daga cikin dubu ashirin da biyar ke mutuwa sakamakon kamuwa da cutar kyenda wanda ya danganta da dalilai na rashin tsaro sakamakon matsalar Boko Haram da kuma tirjiya da ake alakantawa da addini da al’adun gargajiya.
Uwar gidan gwannan jihar Taraba Barr. Ana Darius Dickson Ishaku ta ce akwai bukatar sadaukar da kai a bangare jami’an kiwon lafiya mataki na farko dake aiki a yankunan karkara ba tare da la’akari da matsalar yanayi ko kudaden alawus da ake biyansu ba wajen aiwatar da aikinsu don kada su cutar da wadanda ke zaune a kan tsaunuka ko koramu inda ba bu hanyar mota.
Da yake bayanin kaifin matsalar bullar cutar kyenda a yankunan karkara, sakataren kungiyar shugabannin kananan hukumomi ta kasa reshen jihar Taraba Hon. Idi Mali ya fadawa Muryar Amurka cewa ana samun karuwar mutuwar yara a cibiyoyin kiwon lafiya mataki na farko a ‘yan kwanakin nan sakamakon bullar cutar.
Kan gudumMawar da ya dace sarakunan gargajiya su bayar wajen yaki da cutar, Galadiman Muri Alhaji Lamido Abba ya ce zasu yi yekuwa sako-sako da lugu-lungu har sai sun tabbatar talakawansu sun ruguni shirin allurar rigakafin cutar.
Alkalumar da asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya, MDD, sun nuna an samu karuwar kamuwa da mace macen yara ‘yan kasa da shekara goma daga miliyan dari da casa’in a 2014 zuwa miliyan dari biyar da ashirin da bakwai a 2016 wanda a bana ake kiyasar na iya dara hakan
Saurari karin bayani a rahoton Sanusi Adamu.
Your browser doesn’t support HTML5