Cutar kwalara ta kashe mutane hamsin a jihar Nija

Wata mata da tana fama da cutar kwalara

Rahoton kiwon lafiya a jihar Nija tace mutane hamsin sun mutu bara ta dalilin cutar kwalara.

Rahoton kiwon lafiya a jihar Nija ta Najeriya na nuni da cewa kimanin mutane hamsin suka mutu bara ta dalilin cutar kwalara.

Kwamishinan lafiya na jihar Nija, Mallam Yahaya Dan-Sallau, ya bayyana cewa,gwamnatin jihar ta kiyasta kashe Naira miliyan goma domin shawo kan matsalar cutar kwalara da tayi sanadin mutuwar mutane hamsin a watan Yuni.

Kwamishinan ya bayyana haka ne bayana kamala taron majalisar zartaswar jiha a Minna.

Kwamishina DanSallau ya bayyana cewa, za a yi amfani da Naira miliyan biyar wajen sayen magunguna yayinda sauran kudin kuma zai tafi wajen gudanar da allurar rigakafi da kuma ilimantar da al’umma.

Ya kara da cewa, gwamnatin jihar ta kuma sayi manyan motoci kirar Hilux ta rarrabawa kananan hukumomin da suke kan iyaka domin taimaka masu ci gaba da yaki da cutar polio.

Jihar Nija na daya daga cikin jihohin arewacin Najeriya da rahoton cibiyar kiddiga ta kasa ya nuna cewa, tana kan gaba a fannin matsayin halin rayuwar al’umma yayinda rahoton ya nuna cewa sama da kashi sittin bisa dari na al’ummar kasa na fama da talauci.