Cutar Kwalara Ta Kashe Mutane Da Dama A Kasar Kamaru

Wadansu yara dake fama da Cutar Kwalara

Cutar kwalara ta kashe mutane da dama a kasar Kamaru, yayinda aka kai daruruwa asibitai da dama. Ana fargaban cewa, an shigo da cutar ne a wadansu wurare daga Najeriya, kuma tana iya bazuwa tsakanin ‘yan gudun hijiran dake gujewa tashe tashen hankalin kungiyar Boko Haram.

Arabo Saidou, babban jami’in gwamnati mai kula da harkokin lafiya a yankin arewacin kasar Kamaru yace an fara samun rahoton bullar cutar kwalarar ne a kan iyakar kasar da Najeriya kimanin watanni biyu da suka shige.

Yace cutar tana ci gaba da bazuwa tunda aka sami mutane hudu dauke da cutar a garin Mayo Oulo ke kan iyaka da Najeriya ranar agomas ha takwa ga watan Mayu. Yace mutane da dama, musamman kananan yara, suna mutuwa a ciki da wajen asibitai.

A watan Mayu, Hukumar lafiya ta duniya ta buga rahoto cewa, an sami barkewar cutar kwalara a jihohin Adamawa, Borno da Yobe, tun watan Fabrairu, inda ake kyautata zaton kimanin mutane dubu daya da dari shida da sittin da hudu sun kamu da cutar, mutane talatin da daya kuma suka mutu.

Mutane da dama suna shiga kasar Kamaru daga jihohin Adamawa, Borno da Yobe, domin harkokin kasuwanci. Akwai ‘yan gudun hijira akalla dubu dari a Kamaru da suka kauracewa garuruwansu sakamakon hare haren kungiyar Boko Haram, sama da dubu casa’in kuma suna sansanin ‘yan gudun hijira dake Minawao