An dai soma samun bullar cutar da ke yiwa huhu da hantar dabbobi, musamman na shanu, illa , da ake kira CBPP a turance a wasu rugaye dake yankin.
Alhaji Da’u Leme , ya ce sun yi asarar dabbobi da suka hada da shanu masu dinbin yawa. Cutar yanzu haka na kara yaduwa a wasu sassan jihar ta Taraba. Da’u Leme yace bas u farga ba sai daga baya suka fara yanka shanun kafin suka gano cewa huhun shanun ne ya ke kumbura. Shi kansa ya yi asarar shanu 14.
Wani mutum mai suna Adamu Kaka ya yi hasarar shanunsa kimanin hamsin da biyu sanadiyar wannan cutar. Akwai wani Alhaji da ya yi asarar shanu 70
Dr Lawi John likitan dabbobi dake kula da sashin yaki da yaduwar cututtukan dabbobi a babban asibitin dabbobi na yankin Mambila dake Gembu, ya ce yanzu haka sun soma gangamin fadakar da makiyaya. Ya ce sun samu labarin barkewar cutar a wasu wuraren.
Makiyaya da lamarin ya shafa sun bukaci gwamnatin jiha da ta tarayya su taimaka domin a shawo kan matsalar. Su na bukatar maganin yakar cutar cikin gaggawa.
To sai dai kuma,ga masana irinsu Dr Amos Edgar wani tsohon shugaban kungiyar likitocin dabbobi a Najeriya, na ganin dole hukumomin jihohin da abun ke shafa su tashi tsaye inda ya bada misali da jihar Adamawa da yace tuni suka dauki mataki hana bullar cutar. Y ace kowace shekara ana yin allurai rigakafin cutar. Yace wamnati ta kan sayi maganin cutar a yiwa shanu Rigakafi.
A saurari rahoton Ibrahim Abdulaziz
Your browser doesn’t support HTML5