Cutar Ebola Zata Karu Ninkin -ba-Ninkin a Kasar Liberia

Ma'aikatan kiwon lafiya masu yaki da cutar ebola

Alkaluma da hukumar kiwon lafiya ta duniya ta fitar sun nuna cewa cutar ebola na yaduwa a kasashen uku dake yammacin Afirka musamman a kasar Liberia

Adadin mutanen da cutar Ebola ta halaka a yammacin Afirka ya haura zuwa 2,296, Karin mutane 200 cikin kwanaki hudu da suka wuce.

A sabbin alkaluman da hukumar kiwon ta lafiyar ta bayar jiya talata kan annobar tace jimillar mutane dubu 4 da dari uku ne suka kamu da cutar a kasashe biyar da suke yammacin Afirka.

Kusan rabin wannan adadi na mutanen da cutar ta hallaka ko suka kamu da ita duk a Laberiya suke.Rahoton da hukumar ta bayar jiya gameda Laberiya a ciki tayi gargadin cewa cutar “zata rubanya ninkin- ba- ninkin”, kuma tayi harsashen cewa za a ga Karin dubban mutane da zasu kamu da cutar cikin makonni uku masu zuwa.

Haka kuma hukumar kiwon lafiya ta duniyar tace cutar tana kara “yaduwa sosai” a kasashen Guniea da Saliyo.

Ahalinda ake ciki kuma ba’Amurke na hudu da ya kamu da cutar Eobla a yayinda yake aiki a yammacin Afirka ya iso nan Amurka jiya Talata.Mara lafiyar da ba’a bayyana sunansa ko sunanta ba inda zata ko zai ci gaba da jinya, kamar takwarorinsa da suka gabata.