Hukumomi a Saliyo sun umurci mutane su dakata a gidajensu na tsawon kwanaki uku a wannan watan.
WASHINGTON, DC —
Hukumomi a Saliyo sun umurci mutane su dakata a gidajensu na tsawon kwanaki uku a wannan watan, a matsayin wani bangare na kokarin hana yaduwar cutar Ebola, wadda ta kashe mutane akalla 2,000 a yammacin Afirka.
Mai magana da yawun gwamnatin ya fadi jiya Asabar cewa ba za' a bar mutane su fice daga gidajensu ba, daga daren ranar 18 ga wata zuwa ranar 21 ga wata.
Kungiyar jinkai ta likitoci - Doctors Without Borders - ta yi tir da wannan matakin da cewa zai iya sa mutane su boye bayyana cewa su na dauke da cutar.