Jami’an kiwon lafiya sun ce cutar Ebola ta kashe mutane 14 a yammacin kasar Uganda.
Jami’an kiwon lafiya sun ce cutar Ebola ta kashe mutane 14 a yammacin kasar Uganda.
Wakilin Hukumar Lafiya ta Duniya a Uganda ya bayyana jiya asabar cewa, an sami mutane 20 dauke da kwayar cutar a yankin Kibaale, dake kimanin tazarar kilomita 200 da yammacin Kampala babban birnin kasar.
Darektan ayyyukan kiwon lafiya na kasar Uganda Anthony Mbonye yace suna kokarin tantance mutanen da suka yi cudanya da wadanda da suka kamu da cutar,
Cutar Ebola dai wata cuta ce da bata da magani ko rigakafi, wanda ya kamu da cutar yakan yi fama da zazzabi mai zafi da zubar jinni, kuma cutar tana yaduwa da kuma kisa cikin dan kankanen lokaci.