Jiya ofishin kiwon lafiya na kasar Nijar ya sake fitar da wata sanarwa da ta tabbatar da yaduwar cutar dabbobi da ta kara kashe mutane a yankin Tawa.
Kawo yanzu an samu mutane tamanin da bakwai da suka kamu da cutar. Cikinsu ishirin da bakwai sun rigamu gidan gaskiya sabanin makon jiya inda mutane arba'in da ukku ne aka gano sun kamu da cutar kana ishirin da biyar suka kwanta dama.
Sanarwar tace dalilin cutar ce aka samu karuwar wadanda suka rasu saboda koda aka kaisu asibitoci rashin lafiyarsu ya tsananta basu iya rayuwa ba.Akan haka ne ofishin kiwon lafiya ya kara kira ga al'ummar kasar da su kiyaye matakan riga kafi game da cutar. Matakan kuwa sun hada da daina shan nonon dabbar da ta kamu da cutar ba tare da dafashi ba ko kuma cin naman da bai dahuba sosai. Haka kuma muamala da dabbar da ta kamu da ciwon nada illa ga mutum.
An gargadi duk wanda yake jin zazzabi ya je asibiti cikin gaggawa kada ya bata lokaci saboda akwai maganin ciwon idan an je asibiti da wuri.
Dangane da dabbobi kuma kamar saniya idan ta kamu da ciwon zata yi bari ko kuma ta dinga zawo har ta mutu idan bata samu kula ba. Kamata yayi a shaidawa likitocin dabbobi cikin gaggawa su duba idan cutar ce su bada magani.
Ga rahoton Haruna Mamman da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5