Cutar COVID-19 Barazana Ce Ga Farar Hular Da Ke Yankunan Da Ake Rikici

Sakatare janar din Majalisar Dinkin Duniya ya ce fararen hulan da ke zaune a yankunan da ke yawan fuskantar rikice-rikice na kara fuskantar barazana saboda cutar coronavirus.

A yayin wani taro ta kafar yanar gizo kan yadda za a kare fararen hulla a yankunan da aka faye rikice-rikice, Antonio Guterres ya ce “fararen hula wadanda ke fuskantar rikice-rikice na fuskantar wata sabuwar barazana, mai suna COVID-19.

Ya kuma ce “wannan annobar na kara janyo wa bangarorrin duniya da ke da illoli karin matsaloli.”

Fiye da mutum millian 5.6 a duk fadin duniya sun kamu da cutar yayin da yawan masu mutuwa ya haura dubu dari uku da hamsin.