Musulmai a yankin Sama Maso Gabashin Ghana, wanda ke kunshe da gundumomi 15, ba za su yi layya a babbar Sallar ban aba kamar yadda sauran Musulmai a fadin duniya za su yi ba, saboda yaduwar cutar Anthrax a dabbobi da ta yi kamari a yankin.
Rahotanni na cewa, mutum daya da dabbobi fiye da dari sun mutu a sanadiyar cutar Anthrax din daga gundumomi kimanin shida na yankin. Gundumar Binduri ce ta fi kowacce yawan mace-macen dabbobin, sai gundumar Garu sannan gundumar Bawku ta yamma.
Hukumar lafiya ta Ghana ta ce ba za ta dage haramcin yanka, sayarwa, safara da cin naman shanu, awaki da tumaki daga yankin ba sai an yi wa kashi 70% na dabbobin allurar rigakafin cutar ta Anthrax.
Sai dai kamar yadda dan jarida, Muhammad Zaquwwa ya ce, kwamitin gaggawa kan rigakafin cutar anthrax na yankin ya sanar da su cewa, ana gudanar da allurar rigakafi ga dabbobin yankin, “amma har yanzu ba su iya sun yi wa duk dabbobin ba, kuma a cikin Bawku ma, ba a yi wa ko dabba daya allurar ba”.
Ya kara da cewa, har yanzu haramcin cin naman dabbobi masu kafa hudu na nan.
Babban jami’in lafiyar dabbobi na gundumar Bawku, Fuseini Samson Majeed, ya nuna cewa cutar na da matukar illa ga dabbobi da mutane, kuma idan aka yi sakaci za ta yi wa al’umma lahani.
Yace, dalilin da ya sa ke nan hukuma ta yi hani da yin layya wannan shekarar.
A ranar Juma’a da ta gabata, limaman masallatan Juma’a na yankin sun yi huduba ne a kan mutane su hakura da yin layya bana domin cutar. Muftin garin Bawku, Sheik Khalifa Muhammade Auwal ya gargadi jama’a da su bi dokar da hukuma ta sanya.
Yace, akwai ayyukan addini da yawa da mutum zai samu lada; za a iya yin sadaka da kudin layyan ga mabukata tun da yake larura ce ta hana.
Imurana Madaha Bawku, mazaunin garin Bawku ya nuna cewa jama’a sun amsa kiran malamai kuma sun dauke shi da muhimmaci. Yace, har matasa na yawo gida-gida da suka san ana kiwo, suna ba da shawara kan yadda za a kiyaye daga cutar.
Dr. Patrick Abakeh, Mukaddashin Daraktan Hukumar Kula da Dabbobi (VSD) a karkashin ma’aikatar abinci da noma, ya bayyana cewa, ana aiwatar da matakan shawo kan lamarin.
Ma'aikatar ta raba alluran rigakafi 100,000 ga dukkan gundumomin, kuma mako mai zuwa za a raba 100,000.
Saurari rahoton Idris Abdullah a Sauti:
Your browser doesn’t support HTML5