COVID-19: 'Yan Sandan Kamaru Sun Kori Wasu Masu Ibada A Masallatai

Jami’an ‘yan sanda a kasar Kamaru sun yi amfani da karfi wajen tarwatsa wasu masu ibada a masallatai a yau Juma'a ranar farko a watan Ramadan saboda karya dokar gwamnati ta hana duk wani taron jama'a sakamakon annobar coronavirus. An tabbatar da samun mutane 1,300 dake dauke da cutar coronavirus a kasar da mace-mace 43, Kamaru ce kasar da cutar ta fi shafa a yankin yammacin nahiyar Afrika.

A wata sanarwa, rundunar ‘yan sandan ta ce sun yi amfani da karfi wajen korar wasu musulmai daga akalla masallatai 13 a yankunan yamma, tsakiya, da arewacin kasar, inda masu ibadar suka hakikance akan sai sun yi sallah a lokacin watan Ramadan wanda ya fara a yau Juma’a 24 ga watan Afrilu, duk kuwa da dokar takaita zirga-zirga da hana taron jama'a da gwamnati ta kafa don dakile yaduwar annobar COVID-19.

Awah Fonka, gwanman yammacin yankin Kamaru, ya ce shi ne ya ba ‘yan sanda umurnin yin amfani da karfi wajen koro wadanda da ba sa mutunta doka dake yin sallah a masallatai a garuruwan Foumban, Foumbot da Bafoussam.