A kokarin neman hanyoyin yaki da cutar coronavirus mai shake numfashin bil'adama da ta zama annoba a duniya, wasu matasa biyu a jihar Filato sun gyara wasu na’urorin taimaka wa marasa lafiya shakar numfashi da ake kira Ventilator da turanci, a asibitin kwararru dake jami’ar tarayya a birnin Jos.
Matasan, Williams Gyang da Nura Jibrin Hassan, sun ce duk da shike basu taba ganin na’urar ba, sun gwada basirarsu har suka yi nasarar gyara na’urorin dake da matukar tsada.
Matasan sun kuma yi alkawarin nan gaba in Allah ya yarda, zasu kera na'urorin da zasu taimaka a fannoni dabam daban. Bayan haka sun kuma yi kira ga hukumomin Najeriya da su karfafa gwiwar masu kere-kere a fannin fasaha
Farfesa Francis Uba, likitan yara a asibitin kwararru a jami’ar Jos, ya ce in har hukumomin Najeriya zasu sa ido wajen ganowa da zakulo irin wadannan matasan masu fasaha, to lallai kasar zata ci gaba kamar sauran kasashen duniya.
Saurari karin bayani cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5