Gwamnatoci a fadin duniya na nazarin lokaci da kuma tsarin da ya kamata a bi, wajen gaggauta komawa bakin aiki, ba tare da sun jefa al’umominsu cikin hatsarin kamuwa da Coronavirus ba.
Kasar Spain, ta sassauta dokokin da ta kafa yayin da jami’an gwamnatin Koriya ta Kudu ke cewa suna tattauna yiwuwar samar da sabon tsari da zai sassauta dokar zama a gida.
Spain dai ta bai wa ma’aikatan kamfanoni da bangaren gine-gine damar kowawa bakin aiki, yayin da har yanzu ake fuskantar barazanar yaduwar cutar.
An dai bukaci kamfanoni su bai wa ma’aikatansu kayayyakin kariya, su kuma tabbatar da cewa ma’aikatan na bai wa juna tarazarar mita biyu.
Kasar Spain dai na daya daga cikin kasashen da cutar ta fi shafa, inda mutane sama da 165,000 suka kamu da cutar, kuma mutane 17,000 suka mutu.
Yawancin sassan kasar sun kasance cikin dokar hana fita waje na wata guda.