COVID-19: USAID Ta Tallafawa Jihar Bauchi

Amurka ta jaddada manufarta na ganin cewa ta taimaka wa Najeriya ta kowannne bangare na ci gaba, musamman a bangaren gudanar da ayyukan kiwon lafiya.

Jakadar Amurka a Najeriya, Mary Berth Leonard ta shaida hakan ga gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammed, a lokacin kaddamar da dakin bincike na gaggawa kan cutar COVID-19 a jihar, wanda hukumar raya kasashe ta kasar Amurka (USAID) ta samar.

A tattaunawa ta kai-tsaye tsakanin gwamnan jihar Bauchi Bala Abdulkadir, da kuma jakadar Amurka Mary Berth ta hanyar naurar Telabijin, ta shaida cewa, hukumar USAID ta taimaka wa Najeriya ta bangarori masu yawa na biliyoyin Daloli.

Ta kara da cewar a sanadiyyar bullar cutar Coronavirus, hukumar ta hada hannu da jihohi guda takwas ciki harda jihar Bauchi, domin shawo kan cutar COVID-19.

Gwamnan Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Kauran Bauchi, ya yaba wa gwamnatin Amurka saboda da irin tallafin da hukumar USAID ke baiwa jihar.

Shugaban hukumar ayyuka lafiya a matakin farko Dr. Riwan Muhammed yayi Karin haske game da irin wasu daga cikin ayyukan da cibiyar zata gudanar.

Saurari karin bayani Karin sauti daga Abdulwahab Muhammad.

Your browser doesn’t support HTML5

COVID-19: USAID Ta Tallafawa Jihar Bauchi