Amurka yanzu haka tana da sama da mutane dubu 100,000 da suka mutu sakamakon cutar COVID-19, adadin da ya zarta Amurkawa da suka mutu a yakin Vietnam da Koriya idan aka hada.
Yayin da kasar ta wuce lokaci mafi muni, wasu rukunin ‘yan majalisar dattawa daga bangarorin jam’iyyu biyu na Amurka sun sake sabunta kiran da a yi tsayuwar shiru ranar Litinin don girmama wadanda suka mutu.
Sanata Brian Schatz ya ce, "wajibi ne kasar ta yi alhinin wannan mawuyacin hali mai matukar muni tare da hadin kai da kuma bayyana gaskiyar abin da ke faruwa a wannan lokacin wani bakin ciki da ba mu taba tunanin ba, yana da matukar muhimmaci mu tsaya domin girmama dukan wadanda suka rasa ransu, kana mu yi zaman makoki tare."
"Annnobar COVID-19 ta yi mummunar barna ga kasar mu", Sanata Lisa Murkowski ta fada, "iyalai da dama sun ga yadda wadanda suke kauna ciki wahala. Saboda matakan killacewa masu tsauri, yawanci wadanda ‘yan uwansu suka kamu daga wannan cuta an hanasu zuwa asibiti don yin sallama da su."
A wani kudiri daban a Majalisar Wakilai ma ta yi kira da a rika yin shiru a kullum idan Majalisar za ta gudanar da zama, kazalika da ware rana ta kasa don zaman makoki bayan annobar ta wuce da kuma kafa wani abin tunawa da wadanda abin ya shafa.
Amurka ta sami raguwar yawan wadanda ke mutuwa kullum, amma kuma ci gaban ya sami koma baya a ranar Laraba da aka ba da rahoton sabbin mutuwa dubu 1,400.
A duniya baki daya dai, sama da mutane dubu 355,000 suka mutu daga COVID-19, a cewar kididdigar Jami’ar Johns Hopkins. Akwai kuma kusan mutum miliyan 5 da dubu 700 da suka harbu, tare da kusan kashi 30 bisa dari a Amurka.