COVID-19: Shugaban Ghana Ya Killace Kansa

Shugaban Ghana

Bisa shawarwarin likitoci, daga ranar Juma’a 4 ga watan Yuli Shugaban Ghana Nana Addo Dankwa Akufo Addo, ya fara killace kansa don bin ka’idodin dakile yaduwar cutar COVID-19, a cewar wata sanarwa da Ma’aikatar Yada Labaran Ghana ta fidda.

Shugaban ya zabi yin hakan ne bayan da akalla daya daga cikin wadanda ke kusa da shi ya kamu da cutar COVID-19 a ranar Juma’a.

Ya zuwa yanzu dai Shugaban ba ya dauke da cutar bayan da aka gwada shi, amma duk da haka ya dauki wannan matakin na killace kansa.

A tsawon lokacin da zai kasance a killace, Shugaban zai ci gaba da gudanar da ayyukansa daga Jubilee House fadar gwamnatin kasar, da ke birnin Accra.