COVID-19: NAFDAC ta Ba Masu Maganin Gargajiya Damar Gwada Fasaharsu

Hukumar kula da abinci da magunguna ta Najeriya wato NAFDAC ta ce, ta soma aiki kan sinadirai na magungunan Gargajiya na masana da masu bincike.

A cewar shugabar hukumar, shawarar hakan ta biyo bayan makudan kudade da kasar Madagaska ta nemi Najeriya ta biya don samun maganin gargajiyarta na cutar coronavirus.

Babbar daraktar hukumar Farfesa Mojisola Christiana Adeyeye ta ce hukumar ta baiwa masana da masu binkice damar rejista da kuma bin matakai da hukumar ta tsara a shafinta na yanar gizo don tantance duk wani magani da aka yi don cutar COVID-19.

Ta ce, “za mu gaugauta tantance duk wani magani sannan mu dauki samfurin maganin don mu tabbatar da cewa sun cika ka’idojin hukumar na sarrafa magunguna, kuma ba su da illa ga lafiyar al’umma, za kuma mu bi duk hanyoyin bincike da gwaji kafin a fitar dashi na wasu ‘yan lokuta”.

Shugabar ta kuma kara da cewa, a maimakon Gwamnatin Najeriya ta kashe makudan kudade don sayen maganin gargajiya kan cutar COVID-19 daga kasar Madagascar, kamata ya yi ta yi amfani da kudaden wajen inganta samar da magungunan gargajiya a kasar.

Basarake Ooni na garin Ife, Adeyeye Ogunwusi ya yi Karin bayani akan shirye-shiryen da ya ke na ko-ta-kwana idan hukumar NAFDAC ta tantance samfurin maganin gargajiya da ya mika mata, inda ya ce, a shirye ya ke tsaf tare da tawagar sa a fannin maganin gargajiya domin samawar da ‘yan Najeriya da ma sauran kasashe maganin bayan samun amincewa daga hukumomin gwamnati.

Ya zuwa yanzu dai adadin wadanda suka kamu da cutar ya kai 6,401 a Najeriya, inda aka sallami mutun dubu 1,734 daga asibiti, yayin da mutum dari 192 suka mutu.

Saurari Karin bayani cikin sauti daga Shamsiyya Hamza Ibrahim.

Your browser doesn’t support HTML5

COVID-19: Hukumar NAFDAC ta Baiwa Masu Maganin Gargajiya Damar Gwada Fasaharsu