Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta ce annobar coronavirus na yaduwa a sassan duniya kamar wutar daji.
Hukumomin lafiya sun nuna fargaba kan yadda cutar take saurin yaduwa fiye da yadda aka gani a baya.
Sun lura cewa, cikin wata uku aka samu mutum 100,000 da suka kamu da cutar a duniya, amma kuma cikin kwana 12 kacal aka samu wasu sabbin mutum 100,000 da cutar ta harba.
Shugaban WHO, Tedros Adhanom Gebereyesus, ya nuna matukar damuwa kan wannan sauyi da aka samu game da yadda cutar take yaduwa.
Sai dai a lokaci guda kuma, ya lura cewa, a karon farko tun bayan barkewar cutar, yankin Wuhan da cutar ta fara bulla bai samu wasu sabbin mutane da suka kamu da cutar ba.
A cewarsa, hakan ya nuna akwai kwarin gwiwar za a iya shawo kan cutar duk da irin tsananin da ta yi.