A wata ganawa da manema labarai, Sakataren Gwamnatin jihar Filato, Farfesa Danladi Atu, ya ce yanzu cutar korona na yaduwa ne a tsakanin al’umar jihar shi ya saka gwamnati ta umurci daukacin ma’aikantan jihar da su je don yin gwajin cutar.
Atu ya kara da cewa jihar ita ce ta hudu a jerin jihohin Najeriya da suka fi yawan gwaji, inda ya zuwa yanzu suka gwada mutune 14,861 wanda daga ciki aka samu mutum 982 wadanda suka kamu da cutar, kana 19 suka mutu.
Sannan ya ce bayan wani taro da masu ruwa da tsaki da gwamnatin jihar sun amince da yin sallar Eid-el-Kabir a masallatan juma’a maimakon filin idi da aka saba yi.
Kwamishinan Lafiya na jihar Filato, Dr. Ndam Lar, ya ce ma’aikatan lafiya hamsin da takwas ne suka kamu da cutar korona a jihar, kuma wadannan ma’aikata duka sun kamu da wannan ciwon ne lokaci suke kan gudanar da ayyukansu.
Ya kara da cewa sun dauki mataki na horar da ma’aikatan lafiya a jihar da kuma tabbatar da sun samu kayan aikin da ya kamata.
Hukumomin jihar Filato sun yi kira ga jama’ar jihar da su cigaba da daukan matakan kariya daga cutar korona biros.
Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji:
Your browser doesn’t support HTML5