COVID-19: Kwararru Sun Bukaci Gwamnati Ta Yi Garambawul A Fannin Tattalin Arziki

Kwarraru a bangarori daban daban a Najeriya sun bai wa gwamnatin kasar shawara kan karkatar da akalarta daga dogoro daga arzikin man fetir zuwa wasu fannoni na daban, inda suka bayyana irin matakan da ya kamata a bi wajen tada komadar tattalin arzikin kasar bayan an yi nasarar yaki da cutar COVID-19, musamman a yanzu da gwamnatin ta kara sassauta matakan yaki da cutar.

Masana sun bayyana halin kaka-na-kayin da cutar coronavirus ta kara jefa harkokin da suka shafi tattalin arzikin Najeriya musamman idan aka yi duba da batun da ya shafi ci gaba mai dorewa wanda dukkan kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya a shekarar 2015 su ka dauki alwashin kawo wa wato muradun SDGs, don yaki da talauci, da kare duniya, da kuma tabbatar da cewa al’umma sun ci moriyar zaman lafiya da ci gaba kafin shekarar 2030.

Sai dai tsaikon da annobar ta janyo ga tallalin arzikin kasar wajen cimma wannan manufa na barazana ga ayyukan dubban mutane a fannoni da dama na Najeriya.

Darekta Janar na ofishin kasafin kudaden shigar Najeriya Ben Akabueze, ya ce kashi 20 cikin 100 ne kawai na kudade ke shiga kasar.

Shi kuma Dr. Isa Abdullahi Malami, mai sharhi kan tattalin arzikin kasa a jami’ar Kashere ta jihar Gombe a Najeriya ya ce kasar na bukatar daura dammara da kuma inganta wasu hanyoyin shigar kudadenta baya ga dogaro ga arzikin man fetir da ta yi.

A na shi bangaren Dakta Abdulhakeem Garba Funtuwa, masani kuma mai sharhi kan harkokin da suka shafi kasa da kasa, ya ce kamata ya yi gwamnati ta ringa ba kamfanonin kasar manyan ayyuka na tsare-tsare da gine-gine don karfafa musu gwiwa maimakon ba kamfanonin kasashen waje. A cewarsa, hakan zai taimaka wajen samar da kudade ga gwamnati.

Cikin abubuwan da ke ci wa al’ummar kasar tuwo a kwarya da kuma hana ruwa gudu shine batun cin hanci da rashawa wanda a wannan lokaci da alkaluman annobar cutar COVID-19 ke dada hawa a kasar, ana zargin wasu jami’an gwamnati da yin amfani da damar wajen karkatar da kudaden tallafin da aka ware domin kai dauki ga marasa karfi a kasar.

Kwarrarun sun kara da cewa idan har gwamnatin Najeriya ba ta yi taka-tsan-tsan wajen canza dabarunta ba, lallai kasar ba za ta yi saurin fita daga kangin kalubalen koma baya da cutar COVID-19 ta janyo ba.

Saurari karin bayani a cikin sauti daga Shamsiyya Ibrahim:

Your browser doesn’t support HTML5

COVID-19: Kwararru Sun Bukaci Gwamnati Ta Yi Garambawul A Fannin Tattalin Arziki