COVID-19: Kukan Rashin Samun Tallafin Gwamnati Na Kara Yawa

A sassa daban daban na Najeriya wasu na kokawa kan rashin samun tallafin gwamnati a daidai lokacin da mutane ke zaune a gida sakamakon matakan hana yaduwar cutar coronavirus.

A duk lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi jawabi da tabo batun masaniyar gwamnati game da halin kuncin da talakawa ke ciki sakamakon matakan da aka dauka na takaita harkoki don dakile cutar coronavirus, mutane kan kara baza kunnuwansu don su ji ta inda tallafin da aka sanar zai fito.

Wannan lamarin ya fi ta’azzara a tsakanin wadanda da ma basu da wata sana’a mai kawo musu kudi sai sun fita fafutika, da kuma nakasassu dake dogara ga taimakon taro da sisi.

Hasiyan Bala, na daga cikin mata guragu dake rakube a birnin Abuja, ta ce matukar ba su fito ba to sai dai su kwana da yunwa. Ta kara da cewa har yanzu babu wani tallafi da suka gani kuma takunkumin da aka sanya masu ya ishe su amma idan gwamnati ta bata jari da abinci, ba wanda zai ganta a wurin bara.

Su ma ‘yan kasuwa dake fuskantar matsi a harkokinsu sakamakon matakan na bukatar samun tallafin na gwamnati da zai maye gurbin komada. Adamu Hassan, shi ne shugaban kungiyar ‘yan kasuwar arewa reshen Abuja ya bayyana damuwarsa akan yadda ba a hada da wakilan ‘yan kasuwa a ko daya daga cikin kwamitin yaki da annoba da aka kafa ba. Ya ce abin takaici shi ne babu mambansu ko daya da ya samu tallafin wanda sai dai su ji ana rabo a wani wuri.

Saurari karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

COVID-19: Kukan Rashin Samun Tallafin Gwamnati Na Kara Yawa