COVID-19: Juma'a Hukumomin Kenya Za Su Yi Nazarin Matakan Da Aka Dauka

A yau Juma’a hukumomin kasar Kenya ke shirin sake nazarin ko ana kiyaye matakan da aka dauka don yaki da annobar COVID-19 ko a’a.

Ministan cikin gidan kasar Fred Matiang ya ce cibiyoyin tsaro akan annobar COVID-19 na maida hankali akan matakan da aka sanya a kananan hukumomin Mombasa, Kwale, da Kilifi.

Kasar Kenya na kara kokari wajen sa ido akan jama’a don tabbatar da suna bin dokokin kariya da aka sanya yayin da Shugaba Uhuru Kenyatta ya bayyana cewa jami’an tsaro na kokarin gano wasu mutane 12 da suka tsere daga cibiyar da ake killace masu dauke da cutar COVID-19 a birnin Nairobi.

A yanzu haka dai mutum 320 ne suka harbu da cutar a Kenya, bayan haka an sami mace-mace 14.