COVID-19: Hukumomin Najeriya Sun Yi Gargadi Kan Shan Chloroquine

Gwamnatin Najeriya ta yi gargadin cewa jama’a su guji amfani da maganin Chloroquine don yakar cutar coronavirus, biyo bayan kwantar da wasu mutane uku da aka yi sanadiyar shan maganin fiye da kima, a cewar wani rahoton CNN.

A makon da ya gabata, a yayin ganawa da manema labarai, shugaban Amurka Donald Trump ya ce hukumar tantance magunguna da abinci ta amince da yin amfani da maganin don kauda cutar coronavirus, “An amince da maganin kwarai da gaske, an amince das hi cikin gaggawa, daga masana,” a cewar Trump.

To sai dai kuma hukumar kula da magunguna da abinci ta FDA ta fitar da wata sanarwa jim kadan bayan ganawar ta ce tana zurfafa bincike don ganin ko maganin da aka amince da shi ga cutar zazzabin cizon sauro, za a iya amfani da shi ga mutane masu dauke da cutar COVID-19.

Ko Ma’aikatar Lafiya ta jihar Lagos ta fitar da sanarwar cewa, “Bamu da wata kwakkwarar hujja cewa Kulorokwin na maganin Coronavirus.”

Rahoton CNN ya kara da cewar kudin kwayar ta Kulorokwin ya ninka da kimanin fiye kashi 400% cikin mintuna kadan.