Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi kira ga kasar Pakistan da ta sake daukar matakan killacewa, ganin yadda adadin masu kamuwa da cutar corona ya yi matukar karuwa cikin kwanaki da dama.
A wata wasikar da ya tura ma Ma’aikatar Lafiya ta Punjab, jaha mafi gairma a kasar ta Pakistan, wakilin hukumar ta WHO Palitha Mahipala, ya ba da shawarar da a yi amfani da tsarin killacewar nan na sati biyu, sannan kuma a dada kara yawan wadanda ake wa gwajin cutar zuwa 50,000 a rana.
Wannan kasar dai ta samu masu dauke da cutar wajen 113,702, wadanda su ka mutu kuma sama da 2,100, ciki har da mutane 105 da su ka mutu jiya Talata kawai.
Mahipala ya ce adadin masu dauke da cutar ya karu ne tun bayan da larduna da dama suka sake bude harkokin hada-hada a farkon watan Mayu.