COVID-19: Gwamnatin Kaduna Ta Fara Raba Dubu 20

Gwamnatin Kaduna ta fara rabon tallafin Naira 20,000 domin rage wa mutane radadin dokar zama a gida da aka tilasta wa mutane don a dakile yaduwar Coronavirus.

Gidaje 22,380 ne za su ci gajiyar tallafin wanda aka fara raba wa a jiya Talata.

Ana sa ran kashe jimullar Naira miliyan 446.6 a matsayin tallafin watanni hudu na farkon wannan shekarar.

Wata jami'ar kula da shirin tallafin kudin, Mrs. Saude Amina Atoyebi, ta sheda wa Muryar Amurka cewa za a raba kudaden a kananan hukumomi a jihar da dama.

Ta kuma ce “za a rinka rage yawan wadanda za su shiga karbar kudadensu a lokaci daya domin hana duk wata yawan mu’amala tsakanin mutane.”

Masana tattalin arziki dai na ganin duk da bukatar tallafawa talakawa a irin wannan lokaci, akwai matsalolin da suka kamata gwamnati ta lura da su.

A cewar Dr. Isma'il Mohd Anchau, masanin tattalin arziki kuma malami a kwalejin kimiyya da fasaha da ke Kaduna, “ya kamata a duba wanda ke tsananin bukatar kudin kafin a bayar da su, sannan a sanya ido kan irin hanyar da ake raba kudin.”

Wadannan kudaden dai za a yi watanni hudu ana raba wa mutane su a jihar ta Kaduna.

Saurari wannan rahoton a sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

COVID-19 Gwamnatin Kaduna Ta Fara Raba Dubu 20