Tun bayan bullar mummunar cutar coronavirus a kasashen Afrika gwamnatoci da yawa sun dauki matakai dabam-daban don dakile yaduwar cutar, ciki har da rufe iyakokinsu da kuma rufe wuraren taron jama’a ko cinkoso. Sai dai wasu sun nuna damuwa akan yanayin sansanonin ‘yan gudun hijira inda galibinsu akwai cinkoso.
Jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya, na kewaye da kasashen Afrika guda uku da suka hada da Niger, Kamaru da Chadi kuma an sami bullar cutar coronavirus a wadannan kasashen.
A wata hira ta musamman da Hajiya Yabawa Kolo, shugabar hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Borno, ta ce an dauki matakan kariya sosai a sansanonin, fiye ma da yadda aka dauka a cikin gari.
Duk da cewa an hana zirga-zirga a bakin iyakokin dake yankin, Hajiya Kolo ta ce an ba jami’ai umurnin sa ido sosai akan masu shigowa ta bakin iyakokin da kuma yi masu gwaje-gwaje kamar yadda ake yi a filayen jirgin sama, tare da samun tarihin tafiye-tafiyen da suka yi a cikin ‘yan kwanakin nan.
Hajiya Kolo ta kara da cewa hukumomin jihar na kokarin kafa cibiyoyin killace wadanda suka kamu da cutar coronavirus a wurare dabam-daban, ta kuma kara jaddada muhimmancin kula da tsaftar jiki da ta muhalli da kuma kiyaye umurnin da hukumomi suka daba don dakile yaduwar cutar coronavirus.
A farkon makon nan hukumomi a arewa maso gabashin Najeriya sun dauki matakin hana kai ziyara a sansanonin ‘yan gudun hijirar yankin dake dauke da dubban mutane. Gwamnatin jihar Borno na fatan matakin zai taimaka wajen dakile yaduwar cutar.
Ga karin bayani cikin sauti daga Haruna Dauda.
Your browser doesn’t support HTML5