COVID-19: Fadar Gwamnatin Najeriya Ta Rage Yawan Ma'ikatanta

Tun bayan da Malam Abba Kyari shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Najeriya ya kamu da cutar coronavirus fadar ta shiga halin galari da fargaba. Yanzu dai mataimakin shugaban Najeria farfesa Yemi Osinbajo ya killace kansa tsawon makonni biyu duk da cewa gwajin da aka yi masa ya nuna cewa ba ya dauke da cutar. Tuni kuma jami’an gwamnati da dama suka dauki wannan matakin ganin cewa yawancinsu sun yi hulda da Abba Kyari a kwanan nan.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta fara daukar matakin rage yawan ma’aikatan dake aiki a fadar gwamnati, ciki har da ‘yan jarida da kuma ma’aikatan gwamnatin kasar da mukaminsu bai kai rukuni na 12 ba. Ma’aikatan fadar da zasu iya aiki daga gida an basu umurnin su yi hakan, duk don yaki da yaduwar cutar kamar yadda kudurori na dokokin Najeriya suka tanadar, a cewar Malam Garba Shehu kakakin fadar gwamnatin Najeriya.

Garba Shehu ya kara da cewa ana yin gwaji akan duk wanda ya je fadar gwamnatin Najeriya yanzu kuma ana bukatar duk wanda zai je fadar ya yi amfani da takunkumin rufe hanci da baki kuma dole ya wanke hannunsa.

Yanzu dai an lura cewa ana dari-dari da yin bayanai game da wannan cuta a fadar gwamnatin kasar da wasu rukunnan gwamnati, ganin cewa yawan manyan jami’an dake dauke da wannan cuta ko su ka yi mu’amulla da wadanda ke dauke da cutar suna da yawan gaske a cikin kasar.

Ga Karin bayani a cikin sauti daga Umar Faruk Musa.

Your browser doesn’t support HTML5

COVID-19: Fadar Gwamnatin Najeriya Ta Rage Yawan Ma'ikatanta