CBN Ya Ware Biliyan 50 Wanda Za a Baiwa Mutane a Matsayin Tallafi

Hoton Hedikwatar Babban Bankin Najeriya Da Ke Abuja

Babban Bankin Najeriya CBN, ya sanar da ware Naira biliyan 50 na tallafi wanda zai ragewa alummar kasar raddadi da kuma asarar da suka tafka a sakamakon cutar Coronavirus.

Bankin a karkashin jagorancin Godwin Emefiele ya ce, wadanda za su ci gajiyar tallafin za su kasance magidanta ne da suke gudanar da wasu sana'o'i wanda suka samu koma baya a sakamakon cigaba da yaduwar Coronavirus.

Hakazalika, masu masana'antu da suke da hujjoji kwarara da suka hana su ci gaba da kasuwancin su a sanadiyar hana fita su ma zasu samu tallafin.

Daya daga cikin shugabannin gamayyar kungiyoyin matasan Arewa, Nastura Ashir Sheriff ya ce bai gamsu da yadda za a rarraba wadanan kudade ba.

Ya kuma bayar da shawarar cewa a kasa kudin kashi 37 wato a ba jihohi 36 har da birnin tarayya Abuja sai su raba abinsu domin su ne suka san wadanda za a ba kudin a jihohin su.

Shi kuwa dan Majalisar wakilai a jihar Nasarawa Abdulmumuni Mohammed Ari da ya ce, lallai ya yarda da tsarin rabon jiha jiha, amma yana so a kullum aka fitar da irin wanan kaso, yana kira ga yan Arewa da su nemi cika ka'i'dojin domin su ma su samu tallafin.

Saurarri wannan rahoton a sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

COVID-19: CBN Ya Ware Biliyan 50 Wanda Za a Baiwa Mutane a Matsayin Tallafi