COVID-19: Buhari Ya Ba Da Umurni a Rufe Kano

Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ba da umurnin a rufe jihar Kano da ke arewacin kasar, a wani mataki na dakile yaduwar cutar coronavirus da ta addabi sassan duniya.

Buhari ya ba da umurnin ne yayin jawabin da ya yi wa 'yan kasar a jiya Litinin domin sanar da su matakan da hukukomi ke dauka wajen yaki da cutar COVID-19.

Rahotanni na nuni da cewa, jihar Kano ta samu wasu nau'ukan mace-mace wadanda hukukomi suka ce ba su da nasaba da cutar ta coronavirus.

"Gwamnati ta kafa dokar rufe Kano karkaf dinta gaba daya, nan da sati biyu masu zuwa." In ji Kakakin shugaba Buhari, Malam Garba Shehu yayin da yake tsokaci kan jawabin shugaban.

Ya kara da cewa, "wannan doka da aka kafa mai tsanani a Kano, ina tsammani ba a taba ganin irinta a wasu wuraren ba."

Shehu ya kara da cewa, gwamnatin tarayyar ta dauki wannan mataki ne saboda an ga tasirin da ya yi da aka rufe jihohin Legas, Ogun da kuma Birnin tarayyar kasar.

Amma a halin da ake ciki kuma, gwamnatin tarayyar za ta sassauta dokar da aka saka a wadannan yankuna, "daga nan zuwa sati guda, za a dan fara saussaci ga mazauna wadannan wurare."

Jawabin na shugaba Buhari, ya kunshi sabbin matakan da gwamnatinsa za ta yi amfani da su na bai-daya, ciki har da dokar hana fita tsakanin karfe 9 na dare zuwa 6 na safe a yankunan jihohin.

Amma ‘yan kasa za su samu damar walwalar neman abinci bisa ga ka’ida, don tabbatar da cewa babu zirga-zirga tsakanin gari da gari ko jiha da jiha, sai dai jigilar kayan abinci.

Saurari karin bayani cikin sauti daga Umar Farouk Musa.

Your browser doesn’t support HTML5

COVID-19: Buhari Ya Ba Da Umurnin a Rufe Kano