COVID-19: Bikin Ranar Ma'ikata Na Bana Ba Zai Yi Armashi Ba

Yau Juma’a ake bikin ranar ma’aikata a duk fadin duniya, bikin da ya samo asali tun a lokacin karni na biyu a zamanin daular Romawa

Shekaru aru-aru da suka shude, bikin na ranar ma’aikata da ake kira “May Day” na nufin abubuwa daban daban ga mutane daban daban.

A karni na 18, akan kalli bikin ne ta fuskoki biyu, wato ta fuskar marabtar lokacin bazara da kuma ranar ma’aikata ta kasa-da-kasa, wadda masu ra’ayin kwamnisanci da na gurguzu a Amurka suka dabbaka, domin tuna wani yajin aikin ma’aikata da ya faru a shekarar alif dari takawas da tamanin da shida a birnin Chicago, wanda ya rikide ya koma tarzoma har ya kai ga asarar rayuka.

A nahiyar Turai, duk da dishewar doki da jama’a kan nuna akan bikin gami da kuma annobar coronavirus, akwai kwaryakwaryar bukukuwa da aka shirya za a yi a wasu kasashen nahiyar.
A nan Amurka kuwa, an soke bukukuwa da dama da wasannin da ake yi a titunan unguwanni da suka hada da kade-kade da raye-raye sanadiyyar cutar coronavirus