Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, ya yi gargadin cewa, majalisar na fuskantar babbar jarabawar da ba ta taba gani ba, cikin shekara 75 da aka kafa ta, sanadiyyar barazanar da cutar coronavirus ke yi ga zaman lafiyar duniya, tsaro da kuma fannin kiwon lafiya.
Yayin wani zaman sirri da kwamitin sulhu na majalisar ya yi a jiya Alhamis, Antonio Gutteress ya ce, cutar COVID-19 na kara haifar da tashe-tashen hankula da ke barazana ga matakan da ake so a dauka na yaki da cutar, kamar yadda wata takardar taron ta nuna.
A dai jiya Alhamis ne aka cika kwana 100 da hukumomin China suka sanar da Majalisar bullar wannan cuta, wacce ta haddasa rashin lafiya ga akalla mutum miliyan daya da rabi ta kuma kashe kusan mutum dubu 95.