COVID-19: An Sami Karin Kamuwa A Jihohin Taraba Da Adamawa

COVID-19

Gwamnatin jihar Taraba dake arewa maso gabashin Najeriya ta tabbatar da samun bullar cutar COVID-19 a jihar.

Gwamnan jihar Akitet Darius Dickson Isiyaku ya yi wa al’ummar jihar jawabi ta kafofin yada labarai game da bullar kwayar gutar ta coronavirus, inda ya bukaci jama’a da su kwantar da hankalin su, su kuma kiyaye dokokin kariya da ake ta gargadi a kai.

Ya ce gwamnati za ta yi iya kokarinta wajen ganin ba’a sami yaduwar cutar a jihar ba, kasancewar wadanda aka samu da kwayar cutar mutane ne da suka shigo daga wasu jihohi kuma tuni aka kilade su.

A jihar Adamawa kuwa yanzu haka an samu Karin mutum guda da ya kamu da cutar. Gwamnan jihar Ahmadu Umaru Fintiri ya kafa dokar hana fita tare da kafa kotun tafi da gidanka don hukunta wadanda suka karyar dokar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, DSP Suleiman Yahya Nguroje, ya ce, hukumar ‘yan sanda suna kokarin ganin al’ummar jihar sun killace kan su.

Alkalumman hukumar kula da yaduwar cututtuka ta Najeriya wato NCDC, sun nuna cewa jihohin Cross River, Kogi, Nasarawa da kuma Yobe ne ba a samu bullar gutar ba gawo yanzu.

Saurari Karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

COVID-19: An Samu Karin Mutane A Jihohin Taraba Da Adamawa